Gwamnatin Tarayya zata yi sulhu da 'yan Boko Haram akan 'yan matan Dapchi

Gwamnatin Tarayya zata yi sulhu da 'yan Boko Haram akan 'yan matan Dapchi

- Gwamnatin tarayya ta ce zata bi ta hanyar ruwan sanyi domin ceto 'yan matan Dapchi da 'yan ta'addar Boko Haram suka yi garkuwa dasu

- Ministan harkokin wajen Amurka ya kawo ziyara Najeriya, inda suka yi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari

Gwamnatin Tarayya zata yi sulhu da 'yan Boko Haram akan 'yan matan Dapchi

Gwamnatin Tarayya zata yi sulhu da 'yan Boko Haram akan 'yan matan Dapchi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa tana so ta tattauna da 'yan ta'addar Boko Haram cikin lumana domin ceto 'yan matan Dapchi da suka sace.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a jiya a wata ganawa da suka yi da Ministan harkokin wajen Amurka Mista Rex Tillerson, wanda ya kawo ziyara Najeriya.

DUBA WANNAN: Tashin hankali ba a sa maka rana: Wata tsawa mai karfi tayi sanadiyyar mutuwar mutum 16 a coci

Bayan ganawar da suka yi ta sirri, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa, shugaba Buharin da Mista Tillerson sun yi ganawar sirri inda suka tattauna akan matsalar yaki da ta'addanci, matsalar cin hanci da rashawa, da kuma alakar tattalin arziki da kuma kawo cigaban demokradiyya da ke tsakanin Najeriya da kasar Amurka.

Sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasar, ta bayyana cewa shugaba Buhari ya sanarwa duniya cewa, gwamnati ta amince ta kubutar da 'yan matan da 'yan ta'addar Boko Haram din suka sace cikin ruwan sanyi, domin a samu damar kubutar da su da ransu da lafiyar su.

Mista Tillerson ya yaba da kokarin da shugaba Buhari yake yi na yaki da cin hanci da rashawa, inda ya kara da cewa kudaden da gwamnatin sa ta kwace daga hannun barayin gwamnati, za su taimaka wajen kawo cigaba a kasar tare da karfafa tsaro.

Mista Tillerson ya kara da cewa, ko ta halin kaka Amurka zata cigaba da goya wa Najeriya baya. Sannan kuma zata cigaba da taimakata wurin farfado da tattalin arzikin kasar. Bayan haka kuma zata bada gudunmawa wurin zaben da za ayi na shugaban kasa a 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel