An koma a wofi: Matashi mai shekara 20 a Duniya ya hallaka kan sa

An koma a wofi: Matashi mai shekara 20 a Duniya ya hallaka kan sa

- Wani Bawan Allah ya kashe kan sa da kan sa a Jihar Jigawa

- Wannan mummunan abu ya faru ne a cikin Garin Hadejiya

- Saurayin mai suna Umar shekarun sa 20 da haihuwa a Duniya

Mun samu labari cewa wani Matashi mai shekaru 20 a Duniya da haihuwa ya hallaka kan sa da kan sa. Sunan wannan mutumi Umar Muhammad kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust.

Umar Muhammad ya wanda ke zaune a Unguwar Khandahar a cikin Karamar Hukumar Hadejiya ya kashe kan sa da kan sa ne inji Jami’in da ke magana da yawun bakin ‘Yan Sanda a Jihar watau SP Abdu Jinjiri.

KU KARANTA: Allah sarki: Tsawa ta kashe wasu mutane 16 a coci

Abdu Jinjiri ya bayyana wannan ga manema labarai a Garin Dutse a jiya Litinin. ‘Yan Sandan sun gano gawar wannan mutum ne da yamma a Ranar Lahadi inda aka same shi ya rataye kan sa a gefen wani ruwa.

Bayan haka ne aka garzaya da wannan Bawan Allah zuwa asibiti amma ko da aka isa sai aka ji cewa ya cika. Yanzu dai jami’an tsaro sun fara binciken musababbin mutuwar wannan Bawan Allah wanda ya jawo takaici.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel