Sanata Abdullahi ya janyo hankalin abokan aikin sa kan yiwa gwamnatin Buhari zagon kasa

Sanata Abdullahi ya janyo hankalin abokan aikin sa kan yiwa gwamnatin Buhari zagon kasa

- Sanata Abdullahi Adamu, ya shawarci abokan aikinsa da suyi kokarin bada gudunmuwarsu dan samun nasarar shugabancin Muhammadu Buhari, musamman ‘yan jam’iyyarsu ta APC

- A satin daya wuce ne sanata mai wakiltar Ebonyi daga jam’iyyar PDP, ya zargi Adamu da shirya makarkashiya ta cire shugaban majalissar Dattijai, Bukola Saraki

- Wani jawabi da Adamu yayi a ranar Litinin, yace abun kunya ne ace ‘Yan Majalisar Dattijai ne suke yiwa shugaban kasa makarkashiya

Sanata Abdullahi Adamu, ya shawarci abokan aikinsa da suyi kokarin bada gudunmuwarsu don samun nasarar shugabancin Muhammadu Buhari, musamman ‘yan jam’iyyarsu ta APC maimakon nuna kasawarta.

A wata sanarwa da Mista Adamu ya fitar ranar Litinin, ya ce abin takaici ne yadda wasu 'Yan Majalisar suke yi wajen dakile kokarin na shugaba Muhammadu Buhari.

Sanata Abdullahi ya janyo hankalin abokan aikin sa kan yiwa gwamnatin Buhari zagon kasa

Sanata Abdullahi ya janyo hankalin abokan aikin sa kan yiwa gwamnatin Buhari zagon kasa

Abdullahi Adamu, wanda a watan daya wuce ne aka cireshi daga matsayin shugaban ‘yan Majalissar Dattijai na Arewa, a satin daya wuce sanata mai wakiltar Ebonyi daga jam’iyyar PDP, ya zargeshi da shirya makarkashiya ta cire shugaban majalissar Dattijai, Bukola Saraki, daga kujerarsa.

DUBA WANNAN: Mutum 4 sun mutu sakamakon harin da makiyaya suka kai a jihar Ebonyi - 'Yan sanda

A wani jawabin da yayi cikin sauri ya karyata zargin da ake masa na cewa yana kokarin hambare kakakin majalisa Bukola Saraki daga mukamin sa, inda ya bayyana cewa Saraki a matsayin 'da yake a gareshi.

Ya kuma kara da cewa "sakamakon abubuwan da ‘Yan Majalissar Dattawa suke fada game da gwamnatin mu, ya janyo al’ummar kasar nan sunyi wa shugaban kasa da gwamnatinsa lakabi da ‘go-slow’ a fadar Sanatan".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel