Gwamnatin tarayya ta shirya kawo karshen jinya a asibitocin kasashen waje – Ministan kiwon lafiya

Gwamnatin tarayya ta shirya kawo karshen jinya a asibitocin kasashen waje – Ministan kiwon lafiya

- Ministan harkan kiwon lafiya ya ce gwamnatin tarayya ta shirya kawo karshen jinyar da 'yan Najeriya ke yi a kasashen waje

- Dr Ehanire ya ce shugaba Buhari ya mayar da hankali sa wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya a Najeriya

Karamin Minitsan harkan kiwon lafiya, Dr Ehanire Osagie, ya ce gwamnatin tarayya zata inganta fannin kiwon lafiyar Najeriya saboda kawo karshen jinya da ‘yan kasar ke yi a asibitocin kasashen waje.

Dr Ehanire Osagie, ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da ayyukan da Cibiyar kiwon lafiya na gwamnatin tarayya a jihar Nasarawa (FMC) ta yi.

Gwamnatin tarayya ta shirya kawo karshen jinya a asibitocin kasashen waje – Ministan kiwon lafiya

Gwamnatin tarayya ta shirya kawo karshen jinya a asibitocin kasashen waje – Ministan kiwon lafiya

Ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya mayar da hankali wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya a Najeriya.

KU KARANTA : Mun fara magana da mayakan kungiyar Boko Haram akan sako ‘yan matan Dapchi - Buhari

A jawabin sa ya ce ‘yan Najeriyan dake zuwa kasashen Indiya, Masar, Amurka da sauran su jinya gannin za su mutu idan suka je asibitocin Najeriya.

“Shi yasa gwamnatin tarayya take kokarin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a kasar saboda 'yan Najeriya su daina zuwa kasashen ketare jinya,” Inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel