Turawan dake satar danyen man fetur a Najeriya sun shiga hannu, duba hotunansu da jiragensu

Turawan dake satar danyen man fetur a Najeriya sun shiga hannu, duba hotunansu da jiragensu

Dakarun sojin ruwa a Najeriya sun cika hannu da wasu turawan kasar Ukraine 16 da ake zargi da satar danyen man fetur a jihar Ribas.

Yanzu haka hukumar EFFC mai yaki da cin hanci da rashawa ta fara binciken wasu turawan kasar Ukraine su 16 da ake zargi da satar danyen man fetur a Fatakwal dake jihar Ribasa.

Turawan dake satar danyen man fetur a Najeriya sun shiga hannu, duba hotunansu da jiragensu

Turawan dake satar danyen man fetur a Najeriya sun shiga hannu

Ana tuhumar turawan da jirgin su: SAN PADRE PIO, mai lambar rijista IMO 9610339 NT 2444, da su ke amfani da shi wajen satar danyen man da kutse cikin Najeriya ba tare da izini ko takamaiman wani dalili ba.

Turawan dake satar danyen man fetur a Najeriya sun shiga hannu, duba hotunansu da jiragensu

Hoton jiraginsu

Wadanda ake tuhumar dukkansu ‘yan kasar Ukraine ne; Vaskov Andriy; Garchev Mykhaylo; Shulga Vladyslav; Orlovkyi Ivan; Skoropupov Andrii; Nadaraia Leonid; Vorohin Andriy; Buriak Maskym; Skok Sergiy; Yakovenko Sergiy; Boiachuk Roman; Shakov Vladyslav; Serebriakov Olehshii; Tsuekanenko Gennadiy, Diachenko Dmytro and Postoiuk Sergii.

DUBA WANNAN: Maryam Sanda ta mayar da martani a kan yamadidi da batun yiwa 'yar ta biki

Dakarun sojin rowan Najeriya sun damke su ne ranar 23 ga watan Janairu na shekarar nan, 2018, yayin wani sintiri da hukumar ke gudanarwa domin yaki da aiyukan ma su satar man fetur a gabar Odudu dake Fatakwal, jihar Ribas.

Turawan dake satar danyen man fetur a Najeriya sun shiga hannu, duba hotunansu da jiragensu

Turawan dake satar danyen man fetur a Najeriya sun shiga hannu

Kaftin a hukumar sojin ruwa, S. W Olurundare, wanda ya mika turawan hannun hukumar EFCC y ace sun kama su ne saboda aikata laifuka a cikin yankin Najeriya na cikin ruwa ba tare da izini ko yin biyayya ga dokar Najeriya ba.

Turawan dake satar danyen man fetur a Najeriya sun shiga hannu, duba hotunansu da jiragensu

Jiragin turawan da aka kama

Za a gurfanar da wadanda ake tuhumar da zarar an kamala bincike a kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel