Tashin hankali ba a sa maka rana: Wata tsawa mai karfi tayi sanadiyyar mutuwar mutum 16 a coci

Tashin hankali ba a sa maka rana: Wata tsawa mai karfi tayi sanadiyyar mutuwar mutum 16 a coci

- Wata tsawa mai karfin gaske ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 16, sannan ta jikkata da dama daga cikin wasu masu bauta a cocin Seventh-Day Adventist dake kasar Rwanda

- Lamarin ya faru a ranar asabar din data gabata a wani gari dake kasar Rwanda

- Hukuma ta tabbatar da mutuwar mutum 16 inda da yawa kuma suka jikkata a kai su asibiti

Tashin hankali ba a sa maka rana: Wata tsawa mai karfi tayi sanadiyyar mutuwar mutum 16 a coci

Tashin hankali ba a sa maka rana: Wata tsawa mai karfi tayi sanadiyyar mutuwar mutum 16 a coci

Kimanin mutum 16 ne suka rasa ransu, yayin da wasu da dama kuma suka jikkata bayan da wata tsawa ta fada wata coci ta Seventh-Day Adventist dake kasar Rwanda, a ranar Lahadin nan data gabata.

DUBA WANNAN: Hukumar JAMB zata bawa dalibai damar rubuta jarrabawa daga gida

Shugaban karamar hukumar, Habitegeko Francois, ya tabbatar da faruwan lamarin, inda ya tabbatar wa da manema labarai cewa mutane 14 ne suka mutu a take a wurin, inda sauran mutum 2 sun mutu daga baya dalilin raunukan da suka ramu a jikin su.

Lamarin ya faru a tsakiyar daren ranar Asabar, a garin Nyarguru dake yankin kudu wanda ya hada iyaka da kasar Burundi, a lokacin da 'yan cocin ke ibada.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa lamarin ya shafi mutum 140 ne, inda a take aka garzaya dasu asibiti da cibiyoyin kiwon lafiya, in da mafi yawancin su sun karba magani kuma an sallamo da yawa gida.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel