Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya yi watsi da dokar canza jadawalin zabe

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya yi watsi da dokar canza jadawalin zabe

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da dokan canza jadawalin zaben 2019 wanda yan majalisa suka samar kwanakin baya.

An samu rahoto daga DailyTrust cewa shugaba Buhari ya bada dalilai uku da rashin amincewa da wannan doka da majalisar wakilan tarayya da kuma na dattawa suka samar.

Labarin da aka samu daga majiya mai karfi ya bayyana cewa shugaba Buhari ya aika sakon rashin amincewarsa ga shugaban majalisan wakilai, Yakubu Dogara, da kuma shugaban Majalisan dattawa, Bukola Saraki.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya yi watsi da dokar canza jadawalin zabe

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya yi watsi da dokar canza jadawalin zabe

Ana sa ran shugabannin majalsun zasu karanta wannan wasika tsakanin yau da ranan Alhamis.

Gabanin yanzu, kungiyoyin fafutuka, manyan lauyoyi da wasu shahrarrun yan Najeriya sun bayyana rashin yardarsu da wannan doka kuma sunyi kira ga shugaba Buhari kada ya sake ya amince da shi.

KU KARANTA: Birane 50 mafi hatsari a duniya

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel