Mutum 4 sun mutu sakamakon harin da makiyaya suka kai a jihar Ebonyi - 'Yan sanda

Mutum 4 sun mutu sakamakon harin da makiyaya suka kai a jihar Ebonyi - 'Yan sanda

- Hukumar ‘Yan Sanda ta tabbar da mutuwar mutane 4 bayan wani hari da Makiyaya suka kai a kauyen Jihar Ebonyi

- Jami'an hulda da jama'a Yan sanda, ASP Loveth Odah, ta fadawa manema labarai cewa mutane uku cikin wadanda aka kashe ‘yan kauyen ne, dayan kuma Makiyayi ne

- Gwamnan Jihar ta Ebonyi, Davi Umahi, ya hana kiwon dabbobi cikin gonakin mutane, ya kuma bayyana irin hukuncin da za'a yiwa wanda ya karya dokar

Hukumar Yan Sanda a ranar Litinin a garin Abakaliki, ta tabbatar da mutuwar mutane 4 bayan wani hari da Makiyaya suka kai a kauyen Onunwakpu karkashin karamar hukumar Izzi, a jihar Ebonyi wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu.

Mutum 4 sun mutu sakamakon harin da makiyaya suka kai a jihar Ebonyi - 'Yan sanda

Mutum 4 sun mutu sakamakon harin da makiyaya suka kai a jihar Ebonyi - 'Yan sanda

Jami'ar hulda da jama'a na rundunar, ASP Loveth Odah, ta fadawa manema labarai cewa mutane uku ne daga cikin wanda aka kashe ‘yan kauyen ne, daya kuma makiyayi ne.

DUBA WANNAN: An kama mutane 145 da ake zargi da hannu wurin fadan makiyaya da manoma

Ta ce hatsaniyar ta fara ne lokacin da wani mutum daga kauyen yaje kai sanuwarsa kiwo cikin gonarsa inda ya tarar da wasu makiyaya da dabbobinsu a cikin gonar, ba wanda ya san takamai-mai abunda ya gudana a tsakaninsa da makiyayan, hayaniyarsu dai ta jawo hankalin jama’a, inda suka tarar da hannuwansa a sassare.

Hatsaniyar ta fara nisa kafin jami'an tsaro suka shanyo kan al’amarin, duk da cewa mutane dayawa sun samu raunuka. Amma dai jami’an Soji sunyi nasarar kama daya daga cikin makiyayan, kuma sun kara shaida ma mutane cewa hakan bazai sake faruwa ba.

Kwanannan gwamnan jihar ta Ebonyi, David Umahi, ya hana kiyon dabbobi a cikin gonakin mutane a jihar. Ya kuma baiyana irin hukuncin dake jiran duk wani manomi ko makiyayi dake tayar da hankalin mutane a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel