An kama mutane 145 da ake zargi da hannu wurin fadan makiyaya da manoma

An kama mutane 145 da ake zargi da hannu wurin fadan makiyaya da manoma

- Yan Sanda sun gurfanar da mutane 124 a gaban kotu wandanda ake zargi da hannu cikin fadan Makiyaya da Manoma

- Shugaba Buhari yace duk wanda aka samu da laifin kisan za’a hukuntashi

- Ance wadanda ake zargin sun kasha a kalla jami’an ‘Yan Sanda 30 wadanda gwamnati ta tura don magance kasha-kashe a fadin kasar nan

Hukumar Yan Sanda ta kama mutane 145 a bangarori daban-daban na kasar nan wadanda ake zargi da hannu a cikin fadan Makiyaya da Manoma, jahohin sun hada da Benuwai, Kaduna da kuma Nasarawa.

Hukumar ‘Yan Sanda ta kama mutane 145 da ake zargi da hannu wurin fadan Makiyaya da Manoma

Hukumar ‘Yan Sanda ta kama mutane 145 da ake zargi da hannu wurin fadan Makiyaya da Manoma

Wata majiya ta kusa da shugaban kasa ta bayyan a ranar Litinin 12 ga watan Maris, cewa kamen na masu laifin anyi shi ne daga watan Janairu shekara ta 2016 zuwa Janairu shekara ta 2018. Wani daya bukaci a boye sunansa, yace mutane 124 sun gurfana a gaban kotu sauran 21 kuma suna na ana bincikensu kafi a gurfanar dasu.

KU KARANTA: EFCC ta garkame asusun bankin wanda tayi wa Jonathan hidimar kamfe a 2015

Yace, yan ta’addan sun kasha a kimanin jami’an Yan Sanda 30 wadanda gwamnati ta tura don magance kashe-kashe fadin kasa. A ranar 5 ga watan Maris, a kalla mutun 24 ne aka kasha; 20 kuma sun bace a kauyuka biyu na karamar hukumar Okpokwu a jihar Benuwai, a wani sabon hari da ake zargin Makiyaya ne suka kai.

Yan kungiyoyi da suka hada da Miyetti Allah a ranar Litinin, 12 ga watan Maris, sun bayyana matsayinsu a lokacin da shugaba Buhari ke ganawa da Manoma, a jihar Benuwai, sunyi hakan ne domin a samu mafita ta har abada ta magance kasha-kashe da hare-hare a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel