Hukumar INEC na shirin kona dukkan katin zaben da ba'a karba ba kafin zaben 2019

Hukumar INEC na shirin kona dukkan katin zaben da ba'a karba ba kafin zaben 2019

Sabon kwamishinan zaben hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa na jihar Ondo Dakta Rufus Akeju ya bayyana cewa hukumar ta zabe watau Independent National Electoral Commission (INEC) tana nan ta na shirin kona dukkan katin zaben da ba'a karba ba kafin zaben 2019 mai zuwa.

Mista Akeju yayi wannan kwarmaton ne a yayin da yake fira da manema labarai a garin Akure, jiya Litinin inda ya bayyana cewa tuni da hukumar ta dukufa wajen ganin ta wayar wa da mutane kai don su je su anshi katin zaben su.

Hukumar INEC na shirin kona dukkan katin zaben da ba'a karba ba kafin zaben 2019

Hukumar INEC na shirin kona dukkan katin zaben da ba'a karba ba kafin zaben 2019

KU KARANTA: Ali Modu Sheriff ya sha tambayoyi a hannun EFCC

Legit.ng ta samu cewa kwamishin zaben ya kuma bayyana cewa duk da wannan kokarin na hukumar har yanzu a kwai wadanda ba su je suka anshi na su ba don haka ne ma ya ce hukumar ka iya kone su domin magance yiwuwar anfani da su wajen magudin zabe.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a turance a jiya Litinin ta gayyaci tsohon shugaban jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Alhaji Ali Modu Sheriff.

Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa a jiyan an ga Alhaji Ali Modu yana shiga a ofishin hukumar ta EFCC inda kuma bai fito ba sai da aka dauki awonni.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel