Tsugune-ba-ta-kare-ba: Tsohon shugaban PDP Ali Modu Sheriff ya sha tambayoyi a hukumar EFCC

Tsugune-ba-ta-kare-ba: Tsohon shugaban PDP Ali Modu Sheriff ya sha tambayoyi a hukumar EFCC

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da cin hanci da rashawa ta Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) a turance a jiya Litinin ta gayyaci tsohon shugaban jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Alhaji Ali Modu Sheriff.

Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa a jiyan an ga Alhaji Ali Modu yana shiga a ofishin hukumar ta EFCC inda kuma bai fito ba sai da aka dauki awonni.

Tsugune-ba-ta-kare-ba: Tsohon shugaban PDP Ali Modu Sheriff ya sha tambayoyi a hukumar EFCC

Tsugune-ba-ta-kare-ba: Tsohon shugaban PDP Ali Modu Sheriff ya sha tambayoyi a hukumar EFCC
Source: Facebook

KU KARANTA: Dalilin da yasa na bayyana albashin Sanatoci - Shehu Sani

Legit.ng haka zalika ta samu daga mai magana da yawun hukumar ta EFCC Mista Wilson Uwajaren wanda ya tabbatar da hakan inda ya kuma bayyana cewa sun gayyace shi domin ya ansa wasu tambayoyi.

A wani labarin kuma, Sabon kwamishinan zaben hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa na jihar Ondo Dakta Rufus Akeju ya bayyana cewa hukumar ta zabe watau Independent National Electoral Commission (INEC) tana nan ta na shirin kona dukkan katin zaben da ba'a karba ba kafin zaben 2019 mai zuwa.

Mista Akeju yayi wannan kwarmaton ne a yayin da yake fira da manema labarai a garin Akure, jiya Litinin inda ya bayyana cewa tuni da hukumar ta dukufa wajen ganin ta wayar wa da mutane kai don su je su anshi katin zaben su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel