Matasa sun huro wuta Shugaba Buhari ya rage shekarun takara a Najeriya

Matasa sun huro wuta Shugaba Buhari ya rage shekarun takara a Najeriya

- Wasu Kungiyoyi na matasan Najeriya za su shiga Villa yau

- Matasan na nema Shugaba Buhari ya rage shekarun takara

- Majalisa ta amince don haka Shugaban kasa ake jira kurum

Wasu Matasa har kungiyoyi 55 karkashin tafiyar ‘Not Too Young to Run’ na masu fafatukar ganin Matasa sun samu mulkin Najeriya za su shiga Fadar Shugaban kasa a yau dinnan.

Matasa sun huro wuta Shugaba Buhari ya rage shekarun takara a Najeriya

An hurowa Shugaba Buhari wuta a rage shekarun takara

Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan inda tace daya daga Shugabannin kungiyar YIAGA ta Matasan kasar watau Samson Itodo ya bayyana wannan a farkon makon. Matasan za su kutsa har cikin fadar Shugaban kasar na Aso Villa a yau Talatan nan.

KU KARANTA: Sanatan Benuwe ya fadawa Buhari ana fushi da shi

Matasan su na nema ne Shugaban kasar ya sa hannu kan kudirin da zai ba ‘yan shekara kasa da 40 tsayawa takarar kujerar Shugaban kasa. Yanzu dai Majalisa ta rage shekarun da ake bukata na tsayawa takara inda har ‘dan shekaru 25 zai iya zuwa Majalisa.

Wadannan Kungiyoyi dai za su nemi su gana da Shugaban kasar ba tare da wani zanga-zanga ba domin ganin Gwamnatin Tarayya tayi abin da zai taimaki Matasa wanda su ne mafi akasarin ‘Yan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel