Yajin aiki: Shugaba Buhari zai saki Naira Biliyan 8 kwanan nan – Minista

Yajin aiki: Shugaba Buhari zai saki Naira Biliyan 8 kwanan nan – Minista

- A Ranar Laraba nan ne Ma’aikatan Jami'a za su janye yajin aiki a kasar

- An yi kusan watanni uku ana yajin aiki a Jami’o’in Gwamnatin Tarayya

- Sauran Ma’aikatan Jami’a sun nemi Gwamnati ta biya su wasu Biliyoyi

Bisa dukkan alamu Sanata Chris Ngige wanda shi ne Ministan kwadago na kasar nan ya cin ma matsaya da Ma’aikatan Jami’a da ke yajin aiki tun bara bayan wani taro da aka yi a Garin Abuja.

Yajin aiki: Shugaba Buhari zai saki Naira Biliyan 8 kwanan nan – Minista

Ma’aikatan Jami’o’i za su janye dogon yajin aiki

Chris Ngige ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai biya Ma’aikatan Makarantun jami’ar wasu Naira Biliyan 8 domin kawo karshen wannan yajin aiki. Yanzu haka Kungiyoyin NASU da SSANU da NAAT duk su na yaji tun bara.

KU KARANTA: Fursunoni 150 su ka hardace Al-Kur'ani a Jihar Gombe

Ministan kasar Ngige da kuma karamin Ministan ilmi Farfesa Anthony Anwukah su ka sa hannu a takardar yarjejeniyar inda a bangaren Ma’aikatan Gwamnatin kuma Shugaban NAAT da kuma Kungiyar SSANU da Sakataren NASU su ka sa hannu.

A cikin wannan kudin da za a saki, za a biya Malaman Jami’a na ASUU na jami’ar Ilorin da ta Nsukka da ba su cikin wadanda aka biya alawus a baya. Ana sa rai a gobe za a janye yajin aikin inda ayyuka za su dawo bakin aiki kamar ba ayi ba a cikin Jami’o’in.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel