EFCC: Ana zargin 'Dan gidan tsohon Ministan Abuja da satar sama da Biliyan 1

EFCC: Ana zargin 'Dan gidan tsohon Ministan Abuja da satar sama da Biliyan 1

- EFCC na zargin yaron wani tsohon Minista da laifin sata

- Yanzu haka ana ta shari'a a gaban babban Kotun Tarayya

- Alkalin mai shari’a ya dage shari'ar sai karshen watan gobe

Mun samu labari cewa jiya ne aka zauna a Kotun Tarayya da ke Abuja inda ake zargin 'Dan gidan tsohon Ministan Birnin Tarayya Abuja watau Bala Muhammad da satar kudi har sama da Naira Biliyan 1.

EFCC: Ana zargin 'Dan gidan tsohon Ministan Abuja da satar sama da Biliyan 1

An dage shari'ar yaron tsohon Ministan Abuja

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin kasa zagon kasa ta na karar Shamsuddeen Mohammed da wasu da karkatar da wasu Naira Biliyan 1.1 lokacin Mahaifin sa yana Minista a Gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

KU KARANTA: Buhari ya fada mana wadanda su ka yi sata a Turai - Shehu Sani

Barista Ben Ikani wanda shi ne Lauyan da ke kara ya cigaba da kawowa Kotu shaidar sa. Shi kuwa babban Lauyan da ke kare yaron Ministan Barista Gordy Uche yace hujjar da EFCC ta ke kawowa ba su isa shaida ba a dokar kasa.

Kamar yadda manema labarai su ka rahoto yanzu dai an dage wannan shari'a har sai 24 ga watan Afrilu inda ake karar yaron Ministan da wasu kamfuna 4 da wawure makudan kudi a Abuja a lokacin mulkin tsohon Shugaba Jonathan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel