Amurka ta nemi ni da Jonathan mu bi a hankali a 2015 kuma haka aka yi - Buhari

Amurka ta nemi ni da Jonathan mu bi a hankali a 2015 kuma haka aka yi - Buhari

- Shugaban kasa Buhari ya bayyana yadda su kayi da Amurka a 2015

- Shugaban kasar yace za kuma ayi zaben kwarai a Najeriya a badi

- Gwamnatin Amurka ta yaba ta kuma ce za ta taimakawa Najeriya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Sakataren Gwamnatin kasar Amurka watau Rex Tillerson a fadar Shugaban kasa da ke babban Birnin Tarayya Abuja inda ya bayyana abin da ya faru lokacin zaben 2015.

Amurka ta nemi ni da Jonathan mu bi a hankali a 2015 kuma haka aka yi - Buhari

Abin da kasar Amurka ta fada mana a zaben 2015 inji Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ta bakin mai magana da yawun sa Femi Adesina ya bayyana cewa daf da lokacin zaben 2015, Sakataren Gwamnatin Amurka a wancan lokacin John Kerry ya nemi ganawa da manyan 'Yan takarar Shugaba Jonathan da Buhari.

KU KARANTA: Shehin Malamin addini ya soki Shugabannin Najeriya

Amurka a lokacin ta nemi Shugaban kasa a lokacin Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari da su bi a hankali game da zaben kuma haka aka yi ba tare da an tada fitina ba. Shugaban kasa Buhari ya kuma yi alkawarin za ayi zabe nagari a 2019.

Shi kuma Sakataren Gwamnatin na kasar Amurka Tillerson ya yabawa kokarin da Shugaban Najeriyar yake yi na yaki da rashin gaskiya a Kasar inda yace Amurka za ta taimaka masa. Buhari yace ana amfani da kudin da aka karbe ne wajen gina kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel