Wata Sabuwa: Sai matafiya sun biya kudi kafin su yi amfani da bandaki a filin jirage na Kano

Wata Sabuwa: Sai matafiya sun biya kudi kafin su yi amfani da bandaki a filin jirage na Kano

- Matafiya sun bayyana mamakinsu da sabuwar dokar biyan kudi kafin amfani da bandaki a filin jirage sama na Kano

- Hukumar filin jirgin saman na karbar kudi kafin a ajiye mota bayan kudin da ake biya kafin a shigo harabar jirgin da mota

- Wani ma'aikacin jaridar Vanguard da ya yi basaja a matsayin fasinja ya samo jerin cajin da ake yi kafin amfani da bandaki a filin Jiragen

Wani rahoton bin kwakwkwafi da jaridar Vanguard ta gudanar ya tabbatar da cewar sai matafiya sun biya kudi kafin su yi amfani da bandaki a filin tashi da saukar jirage na Mallam Aminu Kano dake birnin Kano.

Kazalika hukumar filin jirgin saman na karbar kudin ajiye mota bayan kudin da ake biya kafin shigowa harabar filin tashin jiragen.

Wani ma'aikacin jaridar Vanguard da ya yi basaja a matsayin matafiyi ya tabbatar da faruwar hakan.

Wata Sabuwa: Sai matafiya sun biya kudi kafin su yi amfani da bandaki a filin jirage na Kano

Filin jirage na Kano

Ma'aikacin ya bayyana cewar duk da rashin tsafta da kyawun yanayi da bandakan filin tashin jiragen ke ciki, an ajiye wani garjejen mutum a bakin kofa dake karbar kudi kafin mutum ya samu damar yin amfani da bandaki.

DUBA WANNAN: Abubuwa 8 da ya kamata ku sani a kan sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

A rubuce a kofar shiga bandakan filin jiragen, an rubuta baro-baro cewar, ga duk mai son amfani da bandaki domin fitsari sai ya biya N20, bahaya N50, wanka N100.

A ranar Juma'a saida aka hana wani babban jami'in gwamnatin jihar Kano amfani da bandakin saboda rashin canji da zai bayar kafin yin amfani da bandaki.

Wannan sabon tsari na filin tashi da saukar jirage na Kano ya bawa matafiya matukar mamaki domin kusan duk duniya babu inda ake yin hakan.

Duk kokarin jaridar Vanguard na jin ta bakin jami'an gwamnati dake kula da filin tashin jiragen ya ci tura.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel