Abubuwa 8 da ya kamata ku sani a kan sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani a kan sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

- A yau ne ofishin jakadancin amurka dake Najeriya ya sanar da cewar sakataren wajen Amurka zai ziyarci Najeriya a yau, a cigaba da rangtadin kasashen Afrika da yake yi

- A yayin ziyarar ta sa ana saka ran Tillerson da shugaba Buhari za su tattauna batun tsaro da tattalin arziki da kuma karfafa danganataka tsakanin Najeriya da Amurka

- Gabanin ziyarar sa, Tillerson, ya gargadi Najeriya da shugabannin kasashen Afrika a kan ranto kudi daga kasar China

A yau ne ofishin jakadancin kasar Amurka dake Najeriya ya sanar da cewar sakataren wajen Amurka zai ziyarci Najeriya a yau, a cigaba da rangadin kasashen Afrika da yake yi. A yayin ziyarar sa ana saka ran Tillerson da Buhari za su tattauna batutuwan da su ka shafi tsaro da tattalin arziki.

A dangane da wannan ziyara ne, Legit.ng ta gudanar da wani bincike domin sanar da ku wasu abubuwa takwas a kan sakataren wajen Amurka, Tillerson, da ba lallai ku san da su ba.

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani a kan sakataren wajen Amurka Rex Tillerson

Buhari da Rex Tillerson

1. Yana da kusanci da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, domin har karrama shi ya taba yi da kyautar girmamawa ta musamman da kasar Rasha ke bawa mutanen da su ka taimaki gwamnatin kasar.

2. Tillerson ban yarda da batun bayar da ‘yanci ga ma su son auren jinsi ba. Ma su ra’ayin auren jinsi sun soki nadinsa a matsayin sakataren harkokin wajen kasar Amurka

3. Ya ce dumamar yanayi ba barazana b ace ga tsaro duk da cewar ya amince matsala ce dake bukatar a shawo kanta.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun tafka ta'asa a gidan shugaban jam'iyyar PDP da dan majalisa a jihar Kogi

4. Ba burin shi ba ne ya zama sakataren wajen Amurka, y ace matar sat a saka shi karbar mukamin ba tare da son ransa ba.

5. Wannan shine aikinsa na gwamnati na farko. Tillerson na da kwarewa a bangaren kasuwancin duniya kuma ya yi aiki da kamfanin man fetur na Exxon na shekaru ma su tsawo.

6. Ya taba kiran shugaban kasar Amurka, Donald Trump, mutumin banza kafin daga baya ya bayyana cewar Trump mutum ne mai basira. Har yau bai janye wancan kalami nasa ba.

7. Ya kori ma’aikatan ofishin jakadancin kasar Amurka 2,000 tare da rage kasafin kudin da gwamnati ke warewa ofisoshin jakadancin.

8. Kafin nadinsa a matsayin shugaban kamfanin man fetur na Exxon, Tillerson ya kasance abokin hamayyar Donald trump

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel