'Yan bindiga sun tafka ta'asa a gidan shugaban jam'iyyar PDP da dan majalisa a jihar Kogi

'Yan bindiga sun tafka ta'asa a gidan shugaban jam'iyyar PDP da dan majalisa a jihar Kogi

- Gungun wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan shugaban jam'iyyar PDP da tsohon dan majalisar wakilai a jihar Kogi

- Fusatattun matasan sun lalata motoci da dukiya a gidajen shugaban jam'iyyar da ragowar jagororin PDP da su ka kaiwa farmaki

- Tsohon dan majalisar ya ce matasan kwararrun 'yan ta'adda ne tare da yin kira ga jami'an tsaro da su dauki mataki a kansu

Wasu gungun 'yan bindiga sun kai hari gidajen wasu jagororin jam'iyyar PDP da su ka hada da shugaban jam'iyyar da wani tsohon dan majalisar wakilai, Alhaji Abdulkareem Salihu, da wasu ragowar mutum uku a garuruwan Okene, Okehi, da Adavi a jihar Kogi.

A gidan shugaban jam'iyyar, Ogembe, dake kauyen Obehira, 'yan ta'addar sun lalata motocin hawa da dukiyoyin miliyoyin Naira.

'Yan bindiga sun tafka ta'asa a gidan shugaban jam'iyyar PDP da dan majalisa a jihar Kogi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello

Tsohon dan majalisar ya ce 'yan ta'addar sun kware wajen cin mutuncin jama'a da kisan mutane tare da yin kira ga jami'an tsaro da su gaggauta daukan mataki a kansu.

A wani labarin mai nasaba da harin 'yan bindiga da jaridar Legit.ng ta kawo ma ku, mutane uku ne aka tabbatar da sun rasa ransu yayin da wasu 'yan bindiga su ka kai hari kauyen Tandama dake karamar hukumar Danja a jihar Katsina.

DUBA WANNAN: Obasanjo na zawarcin Dogara da Saraki zuwa jam’iyyar SDP

Wani shaidar gani da ido da aka kashe dan uwansa ya ce 'yan bindigar, cikin kakin soji, sun dira a kauyen da misalin karfe 1:15 na safiyar ranar Asabar dauke da bindigu kirar AK 47. 'Yan bindigar sun kai farmaki gidajen Alhaji Safiyanu da Abdullahi Tandama.

Saidai, tirjewar da mutanen kauyen su ka yi tare da tunkarar 'yan bindigar ya yi sanadiyar mutuwar biyu daga cikin 'yan fashin yayin da su ka kashe mutum daya daga mutanen garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel