Mun fara magana da mayakan kungiyar Boko Haram akan sako ‘yan matan Dapchi - Buhari

Mun fara magana da mayakan kungiyar Boko Haram akan sako ‘yan matan Dapchi - Buhari

- Buhari ya ce gwamnatin sa sun fara sulhu da 'yan Boko Haram akan sako 'yan matan Dapchi

- Buhari ya ce baya son ayi amfani da karfin soji wajen ceto yan matan Dapchi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa gwamnatin taraya ta fara tattaunawa da mayakan kungiyar Boko Haram aka sakon ‘yan mata DSS Dapchi dake jihar Yobe da suka sace su a watan da ta gabata.

Shugaba Buhari ya ce, ya fi son a yi sulhu da mayakan Boko Haram fiye da amfani da karfin soji wajen kwato ‘yan matan, saboda yana son ‘yan matan su fito da ran su.

Mun fara magana da mayakan kungiyar Boko Haram akan sako ‘yan matan Dapchi - Buhari

Mun fara magana da mayakan kungiyar Boko Haram akan sako ‘yan matan Dapchi - Buhari

Bayan haka shugaba Buhari ya kara da cewa, gwamnatin sa zata tabbatar da sauran ‘yan matan Chibok dake hannun Boko Haram.

KU KARANTA : Buhari a Benuwe : Kabilar Tiv suna fushi da kai - Akume ya fada wa shugaban Kasa

Idan aka tuna baya Legit.ng ta rawaito muku labarin wani tsohon Daraektan hukumar SSS na jihar Borno, Ahmed Abdullahi, da ya soki gwamnatin tarayya akan yin sulhu da mayakan Boko Haram.

Ahmed Abdullahi, ya ce kuskure ne gwamnatin tarayya ta rika yin sulhu da yarjejeniya da ‘yan Boko Haram, saboda yin haka na kara karfafa su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel