Duniya ina zaki damu ne? Yadda wata Mata ta hallaka wani dan jariri ta jefa gawar cikin masai

Duniya ina zaki damu ne? Yadda wata Mata ta hallaka wani dan jariri ta jefa gawar cikin masai

- Wata Budurwa ta murɗe wuyan jaririn da ta haifa ɗan gaba da fatiha a jihar Sakkwato

- Alkalin Kotun majistri ya yanke mata hukuncin zaman gidan Yari

Rundunar Yansandan jihar Sakkawato sun gurfanar da wata mata mai suna Rabiat Mustapha mai shekaru 30 gaban kuliyan manta sabo kan zarginta da kashe wani dan jariri, ini rahoton The Nation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Rabiat na fuskantar tuhume tuhume guda biyu da suka hada da aikata mugun laifi da kuma hana kisan jariri bayan haihuwa, sai dai ta musanta dukkanin tuhume tuhumen.

KU KARANTA: Yansanda sun cika hannu da wani tsoho mai shekaru 70 da ya kashe wani bahaushe a Ogun

A yayin zaman Kotun, dansanda mai kara Kofur Umar Rabiu ya shaida ma Kou cewa Rabiat wanda ke zaune a unguwar Asada na jihar sakkwato ta aikata wannan laifi ne a ranar 3 ga watan Maris, inda ta murde wuyan dan jaririn da ta haifa ta hanyar samun cikin shege, sa’annan ta jefa gawarsa cikin masai.

Bayan sauraron karar, sai Alkalin Kotun majistri Abubakar Adamu ya bayyana cewar kotunsa bata da hurumin sauraron karar, don haka za garkame Rabiat a Kurkuku, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Afrilu don mika karar zuwa wata Kotun ke da hurumin sauraron karar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel