Yansanda sun cika hannu da wani tsoho mai shekaru 70 da ya kashe wani bahaushe a Ogun

Yansanda sun cika hannu da wani tsoho mai shekaru 70 da ya kashe wani bahaushe a Ogun

Rundunar Yansandan jihar Ogun ta tasa keyar wani tsoho mai shekaru 70, Muyideen Alani gaban wata Kotun majistri dake garin Ota na jihar Ogun kan zarginsa da laifin kisan kai.

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito a zaman Kotun na ranar Litinin 12 ga watan Maris, dansanda mai kara, Inspekta Abdulkareem Mustapha ya shaida ma Kotu cewa suna tuhumar Alani ne da laifin tukin ganganci, wanda yayi sanadiyyar mutuwar Mohammed Lawan.

KU KARANTA: A Najeriyar mu: Yadda wani saurayi mai shekaru 23 ya auri kanwarsa mai shekaru 16

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansandan yana fadin Alani ya tafka wannan aika aika ne a ranar 27 ga watan Feburairu da misalin karfe 8:10 na safiyar ranar a tashar Mota ta Tempo, dake unguwar gonar Obasanjo, a Otta.

Dansandan ya cigaba da fadin; “Direban bankauran yayi tukin ganganci ne a yayin da yake tuka wata motar Tipper na dakon yashi mai lamba KTU 703 XV akan hanyar, inda ya bankade Muhammed Lawan, sa’annan ya tattake shi.”

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dansandan yace laifin da ake tuhumar Alani yaci karo da sashi na 5 da na 13 (1) na kundin dokokin manyan hanyoyin jihar Ogun, na shekarar 2006.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta tuhume tuhumen, daga bisani bayan sauraron dukkanin bangarorin guda biyu sai Alkali Mathew Akinyemi ya bada belin wanda ake tuhumar a kan kudi N500,000.

Haka zalika Alkalin ya bukaci wanda ake tuhumar ya samo mutane guda biyu da zasu tsaya masa, wadanda ke zama a yankin da Kotun majistrin ke zamanta, daga nan kuma y adage sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Mayu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel