Gab da shigan shugaba Buhari Benue, makiyaya sun hallaka yan sanda 2

Gab da shigan shugaba Buhari Benue, makiyaya sun hallaka yan sanda 2

Wasu mutane da ake zargin makiyaya ne sun kai hari Tse Orogbo da ke Nyiev, karamar hukumar Guma na jihar Benue kuma sun kasha yan sanda biyu.

Makiyayan sun kai wannan mumunan hari ne jiya Lahadi, 12 ga watan Maris 2018. Karamar hukumar Guma na daga cikin wuraren da shugaba Buhari zai ziyarta yau.

Yan bindigan sun yi musayar wuta da jami’a yan sanda kusa da wani makarantan Firamare inda suka hallaka yan sanda 2.

Gab da shigan shugaba Buhari Benue, makiyaya sun hallaka yan sanda 2
Gab da shigan shugaba Buhari Benue, makiyaya sun hallaka yan sanda 2

Wani mazaunin unguwar ya bayyanawa manema labarai cewa makiyayan sun yi kokarin kai hari cikin coci ne amma jami’an yan sandan suka karaso.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya isa jihar Benue

Wannan abu ya faru ne yayinda shugaba Buhari ke kokarin kai ziyara jihar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Benue. Shugaban kasan ya dira filin jirgin saman Makurdi misalign karfe 10:43 na safe. Yanzu haka yana gidan gwamnatin jihar inda yake ganawa masu ruwa da tsaki

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel