Gwamnatin jihar Legas ta yiwa makiyaya gargadi

Gwamnatin jihar Legas ta yiwa makiyaya gargadi

- Gwamnatin jihar Legas ta yiwa makiyaya gargadi akan shigo da dabbobi cikin jihar

- Gwamantin jihar Legas ta ce yawo da dabobi cikin jihar zai iya janyo hatsari da kuma yada cututuka

Gwamnatin jihar Legas ta ce dokar hana makiyaya yawo da dabobin a cikin jihar yana nan kuma zata gurfanar da duk wanda ta kama ya saba dokar.

Kwamishinan harkar noma na jihar Legas, Oluwatoyin Suarau, ya bayyana haka a karshen makon da ta gabata a lokacin da yake bibiyar sakamakon rahoto akan dobobin dake yawo jihar ba tare da kulawar ma su shi ba, da kuma masu sufurin dabobi a jihar.

Gwamnatin jihar Legas ta yiwa makiyaya gargadi

Gwamnatin jihar Legas ta yiwa makiyaya gargadi

Sarau ya ce jihar Legas baza ta cigaba da amincewa da irin balao’in da dabobin dake yawo akan manyan titunan jihar ke jawo wa ba, kuma jihar Legas ashirye take ta hana yawo da dabobi a cikin jihar.

KU KARANTA : Hatsarin Mota: Wani direba da yayi tatul da ruwan barasa ya kashe mutane hudu a kofar shiga Lekki (Toll Gate)

Yawo dabbobin da basu da lasisi za su iya janyo hatsari da cututuka kamar, tarin fuka, Cizon kare da sauran su.

Sarau yayi ikrarin cewa gwamnatin jihar Legas na yanzu zata ginawa dabobi hanya na musamman da za a rika bi da su a cikin garin kamar yadda ake da su a kasashen da suka cigaba.

atsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel