Sakataren wajen Amurka zai shigo Najeriya yau, zai gana da shugaba Buhari

Sakataren wajen Amurka zai shigo Najeriya yau, zai gana da shugaba Buhari

Sakataren wajen Amurka, Rex Tillerso, zai gana da shugaba Muhammadu Buhari a ayu Litinin, 12 ga watan Maris, 2018.

Wani kakaki daga ofishin jakadancin Amurka y ace Mista Tillerson zai tattauna da shugaba Buhari.

A cewarsa: “ Tillerson ya kasance babban jami’in gwamnatin Trump da zai kawo ziyara Najeriya. Ana sa ran zai yi hira da manema labarai ranan Talata, 13 ga watan Maris, misalign karfe 11:45 na safe a fadar shugaban kasa.”

Sakataren wajen Amurka zai shigo Najeriya yau, zai gana da shugaba Buhari

Sakataren wajen Amurka zai shigo Najeriya yau, zai gana da shugaba Buhari

Sakataren zai yi mako daya yana yawo a fadin nahiyar Afrika. Ya sanar da cewa Amurka zata bada tallafin 533 million dollars ga Afrika kuma Najeriya da kasashen da yankin tafkin Chadi zasu amfanan da 128 million dollars.

KU KARANTA: Abubuwa biyar da Buhari zai yi a jihar Benuwe a yau

Idan Tillerson ya gana da Buhari, ana sa ran zasu tattauna a kan yadda za’a dakile ta’addanci da kuma tallafawa jama’an yankin Arewa maso gabas.

Kana zasu tattauna kan samar da zaman lafya, tabbatar da tsaro, da kasuwanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel