Abu 1 tak zai iya kawo karshen kungiyar Boko Haram - Obasanjo

Abu 1 tak zai iya kawo karshen kungiyar Boko Haram - Obasanjo

Tsohon shugaban kasara Najeriya na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa kawar da yuwa da fatara tattare da rashin aikin yi ga 'yan kasa ne kadai zai iya kawo karshen ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram.

Cif Obasanjo ya yi wannan ikirarin ne a garin Maiduguri yayin da yake shugabantar wani muhimmin taron tattaunawa domin lalubo hanyar da za'a kai karshen yunwa a yankin domin samun cigaba mai dorewa.

Abu 1 tak zai iya kawo karshen kungiyar Boko Haram - Obasanjo

Abu 1 tak zai iya kawo karshen kungiyar Boko Haram - Obasanjo

KU KARANTA: Jami'an tsaron fadar shugaban kasa sun gudanar da zanga-zanga

Legit.ng ta samu dai cewa muhimmin taron ya samu halartar mai masaukin baki gwamnan jihar Borno Kashim Shettima da kuma tawaga daga ma'aikatar harkokin noma ta tarayya da dai sauransu.

A baya dai mun ruwaito maku cewa Tsohon shugaban kasar Najeriya da ke zaman shugaban kasar na farko a wannan jamhuriyar Cif Olusegun Obasanjo ya isa birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin halartar taron masu ruwa da tsaki da ke da zummar korar yunwa daga Najeriya karo na uku.

Mun samu dai cewa tsohon shugaban kasar ya hadu da ministan ayyukan gona na gwamnatin Buhari Cif Audu Ogbe da ma sauran gwamnonin shiyyar ta Arewa maso gabas domin tabbatar da samun nasarar shirin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel