Yan kabilar Ibo ne za su fi kowa morewa idan Shugaba Buhari ya zarce - Mista Osita Okechukwu

Yan kabilar Ibo ne za su fi kowa morewa idan Shugaba Buhari ya zarce - Mista Osita Okechukwu

Babban darakta Janar na kafar yada labarai ta murayar Najeriya Mista Osita Okechukwu ya bayyana cewa idan ma har shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasarar zarcewa a zaben 2019, to 'yan kabilar Ibo ne za su fi kowa morewa.

Wannan kalaman na shi dai na zuwa ne 'yan kwanaki kadan bayan kungiyar gamayyar 'yan kabilar Ibo din ta Ohanaeze Ndigbo ta fitar da sanarwar cewa su har yanzu ba su yanke hukuncin wanda za su marawa baya ba a zaben 2019.

Yan kabilar Ibo ne za su fi kowa morewa idan Shugaba Buhari ya zarce - Mista Osita Okechukwu

Yan kabilar Ibo ne za su fi kowa morewa idan Shugaba Buhari ya zarce - Mista Osita Okechukwu

KU KARANTA: Sanatoci sun fadi aihafin kudin da suke ansa duk wata

Legit.ng ta samu cewa sai dai shi Mista Osita ya shawarci 'yan uwan na sa na kabilar Ibo da su marawa shugaba Muhammadu Buhari baya domin ta hakan ne kawai za su iya samar da wanda zai gaje shi a shekarar 2023.

A wani labarin kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta gwamnatin tarayyar Najeriya watau Independent National Electoral Commission, INEC a takaice ta sanar da wasu muhimman sauye-sauye a kan yadda za ta gabatar da zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Mun samu cewa hukumar ta zaben ta Independent National Electoral Commission, INEC ta ta bakin kwamishinan ta na jihar Imo Farfesa Francis Ezeonu ya bayyana cewa ba za su yi anfani da fom din nan ba na rubuta kura-kuran da aka samu watau Incident Form.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel