Rashin imani: Yadda Gwamna Bindow ya bada gudummuwa wajen mutuwar mahaifin mu - Iyalan marigayi Saleh Michika

Rashin imani: Yadda Gwamna Bindow ya bada gudummuwa wajen mutuwar mahaifin mu - Iyalan marigayi Saleh Michika

Kimanin 'yan awanni kadan bayan mutuwar tsohon gwamnan jihar Adamawa na farko na farar hula Alhaji Saleh Michika, iyalin sa sun zargi gwamnan jihar na yanzu Muhammad Bindow Jibrilla da bayar da gaggarumar gudummuwa wajen mutuwar ta sa.

A cikin wata kebantacciyar fira da gidan jaridar Daily Trust, daya daga cikin 'ya 'yan san mai suna Abdurrashid Saleh ya bayyana cewa baya ga kin ba mahaifin na su kyakkyawar kulawar da ya kamata daga gwamnati, gwamnan ya kuma ki biyan shi hakkokin sa da suka kai Naira 400 miliyan.

Rashin imani: Yadda Gwamna Bindow ya bada gudummuwa wajen mutuwar mahaifin mu - Iyalan marigayi Saleh Michika

Rashin imani: Yadda Gwamna Bindow ya bada gudummuwa wajen mutuwar mahaifin mu - Iyalan marigayi Saleh Michika

KU KARANTA: Wani tsoho ya sha romon demokradiyya (Hotuna)

Legit.ng ta samu har ila yau cewa iyalan na mamacin sun kuma zargi gwamnan da kin ba shi cikakkiyar kulawar da ta kamace shi musamman ma lokacin da aka bukaci gwamnatin ta kawo muhimman kayan aiki a asibitin tarayya dake a garin Yola.

Sai dai da yake maida martani game da zargin na iyalan mamacin, kwamishinan yada labarai na jihar da kuma tsare-tsare Ahmad Sajoh ya ce sam ba gaskiya ba ne kuma kamata yayi iyalan na mamacin su tambayi yadda lamarin yake ba wai su zargi gwamnatin da kasawa ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel