Abubuwa biyar da Buhari zai yi a jihar Benuwe a yau

Abubuwa biyar da Buhari zai yi a jihar Benuwe a yau

Kamar yadda Legit.ng ta kawo ma ku a labaranta na baya, a yau ne shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki jihar Benuwe mai fama da rigingimu.

Tuni dai shugabanni da jagororin al'umma a jihar su ka hada baki wajen fitar da wasu jerin bukatu da su ke bukatar shugaban ya cika yayin ziyarar ta shi a yau.

Wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan jihar Benuwe a kan watsa labarai, Tahav Agerzua Tahav, ya fitar ta sanar da manyan abubuwa da Buhari zai yi a jihar. Ga biyar daga cikinsu;

1. Buhari zai ziyarci sarki daraja ta daya a jihar Benuwe, Tor Tiv na biyar, Farfesa James Ayatse.

2. Bayan nan zai gana da masu ruwa da tsaki a gidan al'ummar jihar dake birnin Makurdi

Abubuwa biyar da Buhari zai yi a jihar Benuwe a yau

Abubuwa biyar da Buhari zai yi a jihar Benuwe a yau

3. Mutanen jihar Benuwe na bukatar shugaba Buhari ya ziyarci kabarin mutane 73 da su ka ransu a wani rikici da ya faru tsakanin makiyaya da manoma

DUBA WANNAN: Ziyarar Buhari zuwa Benuwe: Jama'ar jihar sun gindaya masa wasu sharuda

4. Kazalika, su na bukatar gwamnatin tarayya ta biya diyya ga jama'ar jihar da rikicin ya jazawa asarar dukiya

5. Su na son ya sake gina garin Agatu da rikici ya lalata.

Tuni aka kara yawan jami'an tsaro a jihar tare da gyara lalatattun hanyoyin jihar da aka san shugaban zai bi ta kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel