Tsoho ya ga Canji: Sai yancu na san ana mulkin Dimukradiyya - Inji wani Dattijon da ya samu aiki a Jigawa

Tsoho ya ga Canji: Sai yancu na san ana mulkin Dimukradiyya - Inji wani Dattijon da ya samu aiki a Jigawa

Dadadden magana ne a yaren Hausa da ake cewa “Ruwan da ya buge ka shi ne ruwa”, ko kuma ace “Da arziki a gidan wasu gara a gidanku”, duk don bayyana cewar mutum ya gamu da alheri.

A nan ma wani dattijo ne mai suna Malam Musa Chakos Mallammadori ya cika da farin ciki a yayin da ya samu aiki da ma’aikatar Ilimi ta gwamntin jihar Jigawa, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

KU KARANTA: Sheƙe aya a bikin Fatima Ganduje: Sheikh Aminu Daurawa ya wanke kansa dangane da zargin kawar da kai

Shi dai Malam Musa Chakos Mallammadori ya samu aikin masinja ne, wato aikin da zai dinga kai sakonni da kuma zuwa ma manyan jami’an ma’aikatar aike da sauran dawainiya.

Tsoho ya ga Canji: Sai yancu na san ana mulkin Dimukradiyya - Inji wani Dattijon da ya samu aiki a Jigawa

Chakos

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Malam Chakos yana fadin duk a tsawon rayuwarsa bai taba shaidawa ana mulkin dimukradiyya a jihar Jigawa ba, tun da dai ruwan da ya buge ka ai shine ruwa.

“Sai yanzu muka san ana mulkin Dimukradiyya a jihar Jigawa, sabanin tsohuwar gwamnatin wacce tayi mana mulki babu adalci balle tausayin mai karamin karfi.” Inji Malam Musa Chakos.

Tsoho ya ga Canji: Sai yancu na san ana mulkin Dimukradiyya - Inji wani Dattijon da ya samu aiki a Jigawa

Chakos

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel