Sojojin Najeriya sun cafke wasu ýan bindiga a cikin ayarin motocin wani ɗan siyasa a jihar Benuwe

Sojojin Najeriya sun cafke wasu ýan bindiga a cikin ayarin motocin wani ɗan siyasa a jihar Benuwe

- Sojojin Najeriya sun cafke yan bindiga guda uku a jihar Benuwe

- Yan bindigan na cikin ayarin motocin wani dan siyasa ne dake takarar dan majalisa

Allah maji rokon bayinsa, ya tona asirin wasu yan bindiga bayan da Sojojin Najeriya suka kama su a karamar hukumar Ankpa na jihar Benuwe daidai lokacin da suke shirin kai hare hare, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.

KU KARANTA: Muhimmin darasi daga wata haduwa da aka yi tsakanin Sheikh Mahmud Gumi da wani Marok

Sojojin Najeriya sun cafke wasu ýan bindiga a cikin ayarin motocin wani ɗan siyasa a jihar Benuwe

Yan bindigan

Jami’an rundunar Sojan Najeriya sun samu nasarar kama wasu mutane guda uku da ake zaton yan bindiga ne dake karkashin wani sanannen dan siyasan jihar Benuwe, inda aka kama su dauke da bindigu da alburusai.

Sojojin sun cafke yan bindigan ne a yayin da suke tsakiyar ayarin motocin wani fitaccen dan siyasa a jihar Benuwe dake takarar kujerar dan majalisa, mai suna John Aduga, inda aka gano bindigu guda biyu, alburusai da kuma wasu kayan sawa.

Sojojin Najeriya sun cafke wasu ýan bindiga a cikin ayarin motocin wani ɗan siyasa a jihar Benuwe

Bindigun

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar yini guda jihar Benuwe don jajanta ma gwamnati da al’ummar jihar bisa hare haren da ake yawan samu a jihar wanda yayi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

Sojojin Najeriya sun cafke wasu ýan bindiga a cikin ayarin motocin wani ɗan siyasa a jihar Benuwe

Motar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel