Munyi takaici: PDP ta mayar da martani bayan da manyanta suka tsere SDP

Munyi takaici: PDP ta mayar da martani bayan da manyanta suka tsere SDP

- Ana qara samun sauyin sheqa daga manyan jam'iyyun kasar nan

- Sau da yawa hakan na zuwa ne daidai loutan da zabuka suka karato

- Makarfi ya mayar da martani bayan ficewar su Jerry Gana

Munyi takaici: PDP ta mayar da martani bayan da manyanta suka tsere SDP

Munyi takaici: PDP ta mayar da martani bayan da manyanta suka tsere SDP

Shugaban Jam'iyyar adawa ta PDP ya bayyana takaicinsa na ficewar wasu manyan siyasa daga jam'iyyarsa ta PDP inda yace wannan abu ne da bayyi masa dadi ba, musamman ganin lokutan zabe na 2019 sun karato.

Wadanda suka bar jam'iyyar dai sun hada da Jerry Gana, da ma wasu manyan jam'iyyar wadanda tun 1998 dasu aka kafa jam'iyyar.

Bayanai da majiyarmu ta samo dai, na nuna cewa yawanci suna ganin jam'iyyar ta rasa tagomashinta ne, saboda gwamna Wike ya mamaye jam'iyyar da ma Ayo Fayose.

Sai kuma masu ganin yawan manyan barayi da aka kama da kudaden talakawa dumu-dumu, wadanda suka sace a lokutan da suke kujerun mulki daga 1999-2015.

DUBA WANNAN: Kwanan nan za'a dankarawa taba da giya tsada a Najeriya

A cewar Makarfi dai, idan ba'ayi hankali ba, wasu manyan ma zasu sake ficewa daga PDP din, su koma jam'iyyar da take ta karbar masu barin jam'iyyunsu zuwa cikinta, watau SDP.

SDP dai ta girmi PDP, kuma itace jam'iyyar da ta ci zabe a lokacin mulkin soji na IBB a 1993, watau jam'iyyar MKO Abiola.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel