Ku saki sunayen 'yan Najeriya masu kadarori a kasashenku - Sanata ya yi kira ga kasashen Turai da Daular larabawa

Ku saki sunayen 'yan Najeriya masu kadarori a kasashenku - Sanata ya yi kira ga kasashen Turai da Daular larabawa

Sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya bukaci kasashen nahiyar Turai da na daular larabawa da su bayyana sunayen 'yan Najeriya dake da kadarori a kasashensu ba kawai su ke sanar da gwamnatin tarayya ba.

Gwamnatin tarayya da kasashen ketare da su ka hada da kasar Birtaniya sun fara musayar takardun biyan haraji na kadarorin da wasu 'yan Najeriya su ka mallaka a kasashensu.

Ku saki sunayen 'yan Najeriya masu kadarori a kasashenku - Sanata ya yi kira ga kasashen Turai da Daular larabawa

Sanata Shehu sani

Sanata Shehu Sani, a shafinsa na Tuwita, ya bayyana cewar ba ya goyon bayan mika sunayen 'yan Najeriya dake da kadarori kasashen ketare ga gwamnatin tarayya. Ya ce kamata ya yi kasashen su buga sunayen wadanda su ka mallaki kadarori a kasashensu domin dukkan 'yan Najeriya su san su.

DUBA WANNAN: PDP zata cigaba da rasa magoya baya - Makarfi

Gwamnatin Najeriya ta sha bayyana cewar zata bukaci sunayen jami'an gwamnati dake da kadarori kasashen ketare daga hukumomin kasashen domin gudanar da bincike a kansu da niyyar gurfanar da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel