Zaben 2019: Za'ayi wa El-Rufai taron dangi - Masu sharhi

Zaben 2019: Za'ayi wa El-Rufai taron dangi - Masu sharhi

- Masu sharhi sun ci zai yi wuya a iya a kawo karshen rigingimun cikin gida da jam'iyyar APC na jihar Kaduna ke fama da shi

- Mafi akasarin 'yan siyasar jihar Kaduna basa tare da El-Rufai

Jihar Kaduna ta daya daga cikin jihohin da jam’iyyar All Progressive Congress APC ke fama da riginginmun cikin gida wanda yaki ci yaki cinye wa.

Gwamnan, Nasiru Ahmed El-Rufai, Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi sun lashi takubban su, suna caccakar juna inda kowa ke ganin shi ke da iko da kuma Jama’a a jam’iyyar.

A Kaduna dai abun da kamar wuya domin tabbas, abin bai sake zani ba daga yadda rikicin ya faro tun bayan rantsar da sabuwar gwamnati a jihar a 2015.

Zaben 2019: Za ayi wa El-Rufai taron dangi - Masu sharhi

Zaben 2019: Za ayi wa El-Rufai taron dangi - Masu sharhi

Abun kamar zai gyaru a wasu lokutan sai gashi ya sake rikicewa yayin da sanata, Suleiman Hunkuyi ya raba jiha da gwamna El-Rufai da ya kai ga har kafa sabuwar ofishin jam’iyyar APC yayi jihar Kaduna.

KU KARANTA : Babu dalilin saka sunan Buhari a titin Filato – Shedrack Best

Tunda man shi, Sanata Shehu Sani sun dade da raba jiha da gwamnan Nasir El-rufai, wanda ko ga maciji basa yi da junan su.

Alamu sun nuna kusan kashi 75% bisa 100% na jiga-jigan yan siyasar jihar Kaduna dake APC, ba sa tare da gwamna El-Rufai, ga kuma jam’iyyar adawa ta PDP suna gefe suna ta shirya yadda za su kwace mulkin jihar daga hannun APC..

Ma su sharhi sun ce lallai akwai shirin yi wa gwamna, El-Rufai, taron dangi. kowa zai tattaro makaman yakin sa ya ja daga da gwamnati mai ci domin ganin an ka da ita. Wasu na ganin har jam’iyyar PDP ma an aika mata da goron gaiyyata wannan buki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel