'Yansandan dake aiki a Aso Rock sun gudanar da zanga-zanga akan rashin biyan alawuns din su

'Yansandan dake aiki a Aso Rock sun gudanar da zanga-zanga akan rashin biyan alawuns din su

- 'Yansanda sun gudanar da zanga-zanga a fadar shugaban kasa

- 'Yansandan dake aiki a Aso Rock sun yi kira da shugaba Buhari ya taimaka ya sa a biya su alawuns din su

Akalla ‘yansanda 53 dake aiki a fadar shugaban kasa na Aso Rock dake Abuja, suka gudanar da zanga-zanga akan rashin biyan alawuns din su, tun daga shekara 2015 da aka tura su aiki a Aso Rock.

Sun yi zanga-zangar ne a takarda korafi d suka aika wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

'Yansandan dake aiki a Aso Rock sun gudanar da zanga-zanga akan rashin biyan alawuns din su

'Yansandan dake aiki a Aso Rock sun gudanar da zanga-zanga akan rashin biyan alawuns din su

‘Yansandan sun ce tunda suka fara aiki a fadar shugaban kasa, suke fama da talauci dan ba a biyan su alawun su din su.

KU KARANTA : Babu dalilin saka sunan Buhari a titin Filato – Shedrack Best

‘Yansandan sun ce shugaban rudunar Squadron da shugaban tawagar dake kula da motocin shugaban kasa, suke hana su samun kudaden su.

“Muna kira ga maigidan mu shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya taimaka ya sa baki a biya mu alawuns din mu saboda mufita daga wahalar da muke ciki,” inji su

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel