Osinbajo, Dolapo, Aisha Buhari sun halarci liyafar Idris Ajimobi a garin Ibadan

Osinbajo, Dolapo, Aisha Buhari sun halarci liyafar Idris Ajimobi a garin Ibadan

Da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya, mun samu rahoton cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo tare da mai dakin sa, Dolapo, uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, sun halarci liyafar bikin Idris da Fatima Ajimobi.

Kamfanin ya kuma ruwaito cewa, gawurtattun 'yan Najeriya sun yi dandazo a Lambun Agodi dake garin Ibadan na jihar Oyo domin taya wannan ma'aurata murna da madangantan su.

Legit.ng ta ruwaito cewa, an dauran auren Idris, dan gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo da Fatima, diyar gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a ranar 3 ga watan Maris a jihar ta Kano wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarta.

Idris Ajimobi da Fatima Ganduje

Idris Ajimobi da Fatima Ganduje

Cikin wadanda suka halarci wannan liyafa a garin Ibadan sun hadar da; gwamna Rotimi Akeredelo na jihar Ondo, Rauf Aregbesola na Osun tare da matar sa, Srifat, Ibikunle Amosun na jihar Ogun da kuma Abubakar Bagudu na jihar Jigawa.

KARANTA KUMA: Ba bu jam'iyyar PDP ba bu kayan ta a jihar Katsina - Oyegun

Sauran wadanda suka halarci liyafar sun hadar da; Alhaji Aliko Dangote, Janar Yakubu Gowon, Asiwaju Bola Tinubu, Cif Femi Otedola, da sauran ministoci da jiga-jigan gwamnatin kasar nan.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma fadar sa ta Villa bayan ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai jihar Filato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel