Babu dalilin saka sunan Buhari a titin Filato – Shedrack Best

Babu dalilin saka sunan Buhari a titin Filato – Shedrack Best

- Mista Shedrace Best ya ce babu dalilin saka sunan Buhari a titin Filato

- Shedrack ya ce tunda Buhari ya hau mulki babu abun da gwamnatin sa ta tsinanawa jihar Filato

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Filato, Mista Shedrack Best, ya soki gwamnan jihar sa,Mista Simon Lalong, akan sanya Titin Maraban Jama’a Sunan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Shedrack Best, ya ce sanya wa Titin jihar Filato sunan, shugba Buhari, kuskure ne saboda babu abun da gwamnatin, shugaba Buhari , ta tsinanawa jihar Filato tun da ya samu mulki.

Babu dalilin saka sunan Buhari a titin Filato – Shedrack Best

Babu dalilin saka sunan Buhari a titin Filato – Shedrack Best

"Banga dalilin da zai sa gwamnati ta saka sunan Buhari a wannan Titi ba, ganin cewa in banda matsaloli da Jihar take fama da su da gwamnatin tarayya bata yi komai akai ba, babu abin da akayi.

KU KARANTA : Mala’iku ne suka hana 'yansanda kama ni a Kotu – Dino Melaye

Best ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidan rediyo jihar Filato, wanda tare da shi akwai kwamishinan yda labaria na jihar Filato, Yakubu Datti, wanda a take a wurin ya kalubalanci maganar da Shedrck yayi akan Buhari.

Datti ya musanta wannan korafi na Best, inda ya ce ”Ko kudin tallafi na ‘Paris Club’ da Buhari ya ba gwamnatin Jihar abin yabo ne domin da ita ne gwamna, Simon Lalong, ya biya lodin bashin albashin ma’aikatan Jihar ake bin gwamnatin Jonah Jang.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel