Shugaba Buhari zai rage zaman kashe wando a Yankin Neja-Delta masu arzikin mai

Shugaba Buhari zai rage zaman kashe wando a Yankin Neja-Delta masu arzikin mai

- Gwamnatin Buhari za ta rage zaman kashe-wando a Kasar Neja-Delta

- Za a samawa Matasa sama da 200, 000 aikin yi a Yankin da ke da fetur

- Hakan zai kawo zaman lafiya ya kuma rage barnar da ake yi a Yankin

Mai magana da yawun bakin Mataimakin Shugaban kasa, Laolu Akande ya bayyana cewa za a samawa jama'a aiki a Neja-Delta. Akande ya bayyana wannan ne bayan wani taro da aka yi a Ranar Juma’a tsakanin Ministocin kasar a fadar Shugaban kasa.

Shugaba Buhari zai rage zaman kashe wando a Yankin Neja-Delta masu arzikin mai

Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari za ta ba matasa aiki

Mista Laoulu Akande yace za a kafa wuraren neman aiki wadanda za su yi sanadiyyar samawa Matasa 208, 000 sana’a a Yankin na Neje-Delta. Hukumar NDDC za ta taimaka wajen cin ma wannan buri na rage yawan masu zaman banza.

KU KARANTA: Peace corps: An nemi Shugaba Buhari ya samawa Matasa aiki

Bayan nan kuma akwai kananan matatu na fetur da za a kafa a irin su Jihar Ribas kwanan nan wanda za su taimakawa matasa wajen samun sana’a. Farfesa Yemi Osinbajo yace wannan zai rage zaman kashe wando a wadannan wuraren.

Haka kuma Laolu Akande ya bayyana cewa Jami’ar koyon harkar ruwa da ke Garin Okerenkoko a Jihar Delta za ta soma aiki a shekarar nan. A watan gobe ne ma ake sa rai cewa za a fara darasi a Makarantar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel