Irin shirin da Atiku yake yi na takarar kujerar Shugaban kasa a 2019

Irin shirin da Atiku yake yi na takarar kujerar Shugaban kasa a 2019

Jaridar Daily Trust tayi sharhi inda ta bayyana yadda Atiku Abubakar yake shiryawa takarar kujerar Shugaban kasa a 2019 ko da har yanzu bai bayyanwa Duniya ba. Atiku yayi kokarin zama Shugaban kasa a 1993, 2007, 2011 da ma 2015.

Atiku ya zo na uku ne a zaben fitar da gwani na Jam’iyyar SDP a 1993. Bayan nan kuma yayi kokarin takarar kujerar a 2003 lokacin da ya ke rike da kujerar Mataimakin Shugaban kasa. Ya kuma sake neman kujerar daga 2007 har zuwa 2015 bai samu ba.

Irin shirin da Atiku yake yi na takarar kujerar Shugaban kasa a 2019

Wazirin Adamawa na kokarin jarraba sa’ar sa a karon karshe

A karshen bara ne Atiku ya fice daga APC zuwa PDP inda yake sa rai zai samu tikitin Jam’iyyar. Kuma yanzu yana ta kus-kus da manyan Jam’iyyar. A shekaru 71 dai kusan wannan na iya zama karo na karshe da Wazirin na Adamawa zai yi takara a kasar.

KU KARANTA: Babu PDP babu kayan ta a Katsina inji Shugaban Jam'iyya

Atiku dai yana da Kungiyoyi burjik da su ke bayan sa wadanda mafi yawan su Matasa ne. Babban ‘dan siyasar na kokarin jawo matasa a jika musamman ta kafafen sadarwa na zamani irin su Facebook da Twitter kamar yadda Donald Trump yayi a Amurka.

Magoya bayan Atiku su na gani shekaru ba matsala bane don kuwa a Amurka ma akwai tsofaffin da ke rike da mulki don haka abin da ake so shi ne karfi da sanin aiki. Bayan nan Atiku na kokarin jawo mutanen Kudancin kasar da kiran sa na yi wa Najeriya garambawul.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel