Jiga-jigan Jam’iyyar PDP sun tsere zuwa wata Jam’iyyar adawa

Jiga-jigan Jam’iyyar PDP sun tsere zuwa wata Jam’iyyar adawa

- Jam’iyyar adawa PDP tayi wani babban rashi a makon da ya gabata

- Manyan kusoshin Jam’iyyar adawar sun tsere zuwa Jam’iyyar SDP

- Hakan dai zai iya kawowa Jam’iyyar cikas a zabe mai zuwa na 2019

Mun samu labari cewa kwanakin baya wasu kusoshi da a Jam’iyyar PDP sun fice daga Jam’iyyar inda su ka sauya sheka zuwa Jam’iyyar SDP. Hakan dai zai iya kawowa Jam’iyyar adawar matsala a 2019.

Jiga-jigan Jam’iyyar PDP sun tsere zuwa wata Jam’iyyar adawa

Wasu manyan PDP sun koma Jam’iyyar adawa ta SDP

Yayin da ake fara shiryawa zaben 2019, Jam’iyyar PDP ta tafka babban rashi ne bayan da wani tsohon Ministan labarai na kasar Farfesa Jerry Gana wanda yana cikin wadanda ake ji da su a PDP ya fice daga Jam’iyyar a makon can da ya gabata.

KU KARANTA: Rikicin da za su fi karfin Tinubu a APC

Farfesa Tunde Adeniran wanda ya nemi takarar Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa kwanan nan shi ma ya bar PDP gaba daya. Haka zalika kuma Farfesa Rufai Alkali wanda yana cikin wadanda su kayi wa Jam’iyyar hidima ya fice zuwa SDP.

PDP dai tace wannan duk a banza.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel