Sarkin Kano ya kalubalanci shugabannin Arewa kan Talauci da Jahilci

Sarkin Kano ya kalubalanci shugabannin Arewa kan Talauci da Jahilci

Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya sake jaddada rashin jin dadin sa dangane da yadda Arewacin Najeriya ta dauki wani salo mara bullewa na rashin ci gaba tare da koma baya a dukkan mu'amalolin su na rayuwa.

Da wannan lamari ne Sarkin yake kalubalantar masu iko da fada a ji na yankin, akan su tashi su farga tare da kawo sauyi na hakika domin inganta rayuwar al'umma.

Jaridar Independent ta ruwaito cewa, Sarkin ya yi wannan batutuwa ne a bikin yaye dalibai na jami'ar jihar Gombe, inda ya jaddada yadda jahilci da kuma talauci suka kai wani munzali na bukatar a shawo kan su a Arewa.

Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II

Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II

A yayin da yakunan Arewa Maso Gabas da Arewa Maso Yamma suka fi yawan adadin mutane da kuma musulmai, sun kuma kasance yankunan da ake yawaitar samun matsaloli da mace-mace a yayin haihuwa da kuma rashin wadataccen ilimi na zamani da kuma aikin yi a yankunan.

KARANTA KUMA: Sarkin Musulmi ya soki ƙwalisar wasu Malaman Addini

Cikin nadama da kuma takaici, Sarki Sunusi yake kira ga masu fada a ji na Arewa akan su tsaya tsayin daka kafin wataran a wayi gari babu wani abin mora ko alfahari a yankin Arewa.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Ministan birnin tarayya ya bayar da kyautar mota da zunzurutun kudi na N500, 000 ga wata daliba da tayi zakakuranci a gasar Al-Qur'ani da aka gudanar makonnin da suka gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel