PDP ta maida martani kan batun juyin mulkin sojin Najeriya

PDP ta maida martani kan batun juyin mulkin sojin Najeriya

- Ike Ikweremadu ne ya fara batun za'a iya juyin mulki a kasar nan

- An kama kaddarori ne a kasashe daban-daban da aka ce nasa ne

- PDP ce ta karbi mulki daga soji a 1999

PDP ta maida martani kan batun juyin mulkin sojin Najeriya

PDP ta maida martani kan batun juyin mulkin sojin Najeriya

Jam'iyyar Adawa ta PDP ta mayar da martani kan irin kalaman da ke fita daga bakin Sanatanta mafi girma a mulkin kasar nan, da cewa kalamai ne da basu dace ba.

Shi dai Sanatan yace a yadda al'amura ke tafiya yanzu, akwai yiwuwar sojoji su sake dawowa su kwaci mulki, kalamai da ake gani kamar yana ma gayyatar sojojin ne su zo su kori 'yan siyasa, bayan da binciken EFCC ya kai kansa kuma aka gano manyan kadarori kasashe daban-daban da aka ce wai nasa ne.

DUBA WANNAN: Abubuwa 13 da ya kamata ku sani game da Afirka

Jam'iyyar ta PDP, wadda tayi mulki tun 1999 zuwa 2015, bayan mulkin sojoji na kusan shekaru 30, tayi kira ga soji da kar su sake su saka rai da sake kwata ko mulkar Najeriya, da ma kiran lallai su yi zaman su a bariki, kuma su bi doka da oda su bar 'yan siyasa su mulki jama'a.

An dai dade ba'a ga juyin mulki ba, domin yanzu ya zama tsohon yayi, tunda kusan duk kasashen Afirka da a da ke karkashin soji yanzu sun koma na mulkin farar hulla.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel