UNICEF ta nemi hadin kan Aisha Buhari wajen kare hakkin yara da mata

UNICEF ta nemi hadin kan Aisha Buhari wajen kare hakkin yara da mata

- Asusun tallafin yara na duniya UNICEF ta roki Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bayar da gudunmawa wajen yaki da gallaza wa yara

- UNICEF tana neman hadin gwiwa da Aisha Buhari wajen nema wa yara wa yara hakin su da kuma inganta ilimi a Najeriya

- Aisha Buhari ta tayi alkawarin cigaba da bayar da gudunmawa wajen yaki da cin zarafin yara da mata a Najeriya

Asusun tallafin yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta nemi hadin kan uwargidan shugaban kasa, Mrs. Aisha Buhari wajen kare hakkin yara da mata da kuma ilmantar da su a Najeriya.

Jakada Hukumar ta UNICEF a Najeriya, Mista Mohammed Fall, yayi wannan rokon ne a ranar Asabar a wata liyafar cin abinci da aka shirya don girmama Aisha Buhari saboda irin jajircewa da ta keyi wajen kare hakkin mata da yara wanda aka shirya a Cibiyar cigaban mata na Najeriya.

UNICEF ta nemi za tayi aiki tare da Aisha Buhari don kawo karshen cin zarafin yara a Najeriya

UNICEF ta nemi za tayi aiki tare da Aisha Buhari don kawo karshen cin zarafin yara a Najeriya

Hukumar ta UNICEF ta bawa Aisha Buhari karrama Aisha Buhari da lambar yabbo na kan irin gudunmawar da ta ke bayar wa wajen yiwu al'umma aiki ta hanyar gidauniyar ta na 'Future Assured'.

KU KARANTA: Riginginmu shida a APC da zasu yiwa kwamitin Tinubu wahalar sulhuntawa

Fall yace ta cancanci lamabar yabon ne idan akayi la'akari da irin gundunwawar da take bayar ga wanda rikicin Boko Haram ya ritsa da su da kuma mata da yara wanda ake cin zallin su a kasar.

Ya kuma koka kan adadin yara da basu da daman zuwa makaranta a nahiyar Afirka kuma hakan yasa ya ke neman goyon baya da hadin gwiwa na uwargidan shugaban kasan.

A jawabin ta tayi, Aisha Buhari ta mika godiyar ta ga Hukumar kuma tayi alkawarin cigaba da yaki da duk wani irin cin zarafi ga yara da mata a Najeriya.

Aisha Buhari, wadda ta samu wakilcin uwargidan kakakin majalisar wakilai, Mrs. Gmbiya Dogara ta bayyana cewa gudunmawar da take bayar wa ya samo asali ne saboda niyyar ta na taimakawa al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel