Gobara ta handame wani babban kamfani a jihar Legas

Gobara ta handame wani babban kamfani a jihar Legas

Mun samu rahoton cewa wani kamfani na kayan roba dake unguwar Ajao ta gundumar Isolo a jihar Legas ya kama da wuta gadan-gadan a ranar Asabar ta yau.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan gobara ta afku ne tun da misalin karfe 2.00 na dare a yayin da ma'aikata ke tsakiyar aiki.

'Yan agaji sun yi gumurzu na kashe wannan gobara da har sai da aka nemi motoci 20 na kwana-kwana wajen cin karfin wutar bayan da ta riga da lashe rabon ta.

Gobara ta handame wani babban kamfani a jihar Legas

Gobara ta handame wani babban kamfani a jihar Legas

Shugaban hukumar kwana-akwana na jihar, Razak Fadipe, shine ya tabbatar da faruwar wannan lamari da cewa, motocin kwana-kwanan na hukumar jihar da na tarayya sun kawo dauki tare da agajin motoci na kamfanin Julius Berger wajen kashe wannan gobara.

KARANTA KUMA: Mutu ka raba: Sirrikan rike miji a gidan aure

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an yi babbar sa'a babu ko rai daya da aka rasa ballanta kuma rauni, sai dai an tafka asarar dukiya sakamakon girman ta'adi da gobarar ta yi a kamfanin.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad III, ya caccaki kwalisar wasu malaman addini da rashin tawali'un su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel