Badakalar zamanin PDP: Kiris, a fara kama wasu manyan kasar nan daga tsofin Gwamnoni da Ministoci

Badakalar zamanin PDP: Kiris, a fara kama wasu manyan kasar nan daga tsofin Gwamnoni da Ministoci

- A jiya gwamnatin tarayya ta bude sabon shafin binciken kudaden da tsofaffin Gwamnoni, Ministoci da Sanatoci suka diba daga asusun gwamnati ba bisa ka’ida ba.

- Babban Janar na tarayya da shugaban hukumar harkokin kasuwanci da tattalin Arziki Mr. Ibrahim Magu sun kama hanya zuwa kasar dubai a daren jiya domin tattaunawa kan yanda za’a maidowa Najeriya dukiyarta da aka diba zuwa kasar tasu ba bisa ka’ida ba.

- Wadanda ake zargi da dibar dukiyar al’umma ba bisa ka’ida ba zuwa wasu kasashe sun kai mutum 20. Duk da dai an boye sunayen mutanen lokacin tattara wannan rahoto

Badakalar zamanin PDP: Kiris, a fara kama wasu manyan kasar nan daga tsofin Gwamnoni da Ministoci

Badakalar zamanin PDP: Kiris, a fara kama wasu manyan kasar nan daga tsofin Gwamnoni da Ministoci

A jiya ne gwamnatin tarayya ta bude sabon shafin binciken kudaden da tsofaffin Gwamnoni, Ministoci da Sanatoci suka diba zuwa kasar Larabawa.Babban Antoni Janar na Tarayya, Mallam Abubakar Malami (SAN), da kuma Shugaban Hukumar EFCC, Mr Ibrahim Magu, sun kama hanya zuwa kasar Dubai a daren jiya domin tattaunawa kan yanda za’a maidowa kasar nan dukiyoyin ta da aka diba ba bisa ka’ida ba.

DUBA WANNAN: Wani Mulhidi a kasar Masar ya gamu da gamonsa

Mutanen da ake zargi da dibar dukiyar al’umma ba bisa ka’ida ba zuwa wasu kasashe sama da mutum 20, duk da dai an boye sunayen nasu a lokacin tattara wannan rahoto.

Najeriya tasa hannu a kan yarjejeniya 6 tsakaninta da kasashen Larabawa, a ranar 19 ga watan Janairu, shekara ta 2016, bayan ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ya kai a Kasashen.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel