Wasu jiga-jigai daga babbar jam'iyya na biki da gangami yanzu haka a Katsina na sauya sheqa

Wasu jiga-jigai daga babbar jam'iyya na biki da gangami yanzu haka a Katsina na sauya sheqa

- Gabanin zabe ana ta sake samun masu sauya sheqa don ayi dasu a 2019-2023

- A Katsina an sami masu sauya sheka a yau dinnan suna taronsu a filin Polo

- A da dai, lokaci mulkin Yaraduwa da yawansu sun shiga PDP ne, amma yanzu APC suke so suyi

Wasu jiga-jigai daga babbar jam'iyya na biki da gangami yanzu haka a Katsina na sauya sheqa

Wasu jiga-jigai daga babbar jam'iyya na biki da gangami yanzu haka a Katsina na sauya sheqa

Su dai jiga-jigan da a da lokacin mulkin PDP a sama da qasa, suke cin moriyarta, yanzu haka sunce wai sun gano gaskiya, don haka so suke su koma biyayya ga shugaba Buhari gabanin manyan zabukan duk kasa da za'a shiga a 2019.

Sun hada da Sanata Ibrahim Ida, Nura Khalil, mai takarar gwamnan jihar daga Karaduwa a baya, da ma tsohon kakakin majalisar jihar Honorabul Gwajo-Gwajo.

Sun kuma ce sun taho da dukkan jama'arsu da suka kai akalla mutum 350,000 izuwa APC domin a dama dasu.

DUBA WANNAN: Wani Mulhidi a kasar Masar ya gamu da gamonsa

A da dai, loacin mulkin PDP da ma kuma mulkin Yar'aduwa, shugaba Buhari bashi da wata fada aji a jiharsa ta Katsina, inda Kano ce kawai ke ganin girmansa a yankin, saura kuwa suka dauke shi sha-ka-tafi.

Mulki dake hannunsa a yanzu ya sa wasu sun dawo suna masa biyayya kamar ba gobe.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel