Sarkin Musulmi ya soki ƙwalisar wasu Malaman Addini

Sarkin Musulmi ya soki ƙwalisar wasu Malaman Addini

A yayin biki na bude gasar Al-Qur'ani ta kasa karo na 32 da aka gudanar a jihar Katsina, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubukar III, ya soki wasu malaman addini da suka dauki salon shiga ta kwalisa yayin bayyana gaban al'umma.

Sarkin ya bayyana damuwar sa dangane da yadda malaman ke holewa ta hanyar shiga tsala-tsalan motoci da kuma kwanciya a gidaddaji na alfarma.

Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, shine ya wakilci Sultan a yayin gasar ta Al-Qur'ani, inda ya bayyana takaicin sa dangane da yadda malamai ke kwalisa a madadin su zamto madubin dubawa ga al'umma.

Sarkin Musulmi ya soki ƙwalisar wasu Malaman Addini

Sarkin Musulmi ya soki ƙwalisar wasu Malaman Addini

A yayin da wannan batu zai bakantawa 'yan kwalisar Malamai, sai dai ko shakka babu gaskiya guda ce kuma daga kin ta sai bata kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, inda ta bayar da misalan magabatan malamai masu tawali'u da kankan da kai.

KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga sun salwantar da rayuka 5 a harin jihar Filato

Duk da cewar bai dace malaman su yi shiga cikin tsumman tufa ba, hakazalika Sultan ya kwadaitar da su romon dake cikin kan-kan da kai tare da tawali'u irin na sunnar Annabi tsira da Amincin su kara tabbata a gare shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel