Ministan Abuja ya bayar da kyautar mota da N500, 000 ga hazikar da ta lashe gasar Al-Qur'ani

Ministan Abuja ya bayar da kyautar mota da N500, 000 ga hazikar da ta lashe gasar Al-Qur'ani

A ranar Juma'ar da ta gabata ne, ministan Abuja Mallam Muhammad Bello, ya bayar da kyautar mota da zunzurutun kudi na N500, 000 ga hazikar da ta lashe gasar haddar Al-Qur'ani ta kasa da aka gudanar makonnin da suka gabata.

Ministan dai ya bayar da kyautar ne ga Maimuna Hussaini, bayan nuna zakakuranci da ta yi a gasar Al-Qur'ani ta bangaren mata.

Hazikar ta lashe gasar Al-Qur'ani ta kasa a karo na 32 da jami'ar Usman Danfodio ta dauki nauyi kuma aka gudanar a jihar Katsina daga ranar 23 ga Fabrairu zuwa 3 ga watan Maris, inda hafizai 156 suka fafata daga jihohi 36 na kasar nan tare da babban birnin tarayya.

Ministan ya kuma bayar da kyautar kwamfuta mai tafi gidan ka ga hazikar, bayan ya gwan-gwaje ta da mota kirar Hyundai samfarin shekarar 2017.

KARANTA KUMA: Bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu, shugaba Buhari ya koma fadar sa ta Villa

Legit.ng ta ruwaito cewa, Maimuna wadda ba ta wuci shekaru 20 a duniya ba, daliba ce a jami'ar Ahmadu Bello dake garin Zaria kuma 'yar asalin gundumar Gwagwalada a birnin Abuja.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, ruwan teku ya kwararo wata jaka dauke da hannayen mutane 54 a kasar Rasha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel