Abinda ya dace gwamnati tayi don shawo kan matsalar ta'addanci - Mama Boko Haram

Abinda ya dace gwamnati tayi don shawo kan matsalar ta'addanci - Mama Boko Haram

- Wata mai kare hakkin dan Adam yar Arewa maso gabas, wadda aka fi sani da Mama Boko Haram, Aisha Wakil ta bayyana abinda gwamnati zatayi don kawo karshen ta'addanci a yankin

- Wakil ta bayyana cewa yan kungiyar Addinin musuluncin sune fushi ne kan yadda jami'an tsaro ke halaka musu 'yan uwa

- Ta shawarci gwamnati ta tsaya tsayin daka ta tura jami’an da zasu iya yin magana da yan ta'addan don a dakatar da hare-haren

Wata mai kare hakkin dan adam wadda aka fi sani da Mama Boko Haram, yar Arewa maso Gabas, mai suna Aisha Wakil ta shawarci gwamnatin tarayya da aike da wakilan da zasu iya magana da yan ta’adda don sun daina kai hare-hare a kasar nan.

Yan ta'adda za suyi sulhu idan an tuntube su - Mama Boko Haram

Yan ta'adda za suyi sulhu idan an tuntube su - Mama Boko Haram

Wakil wadda tace Boko Haram bazasu taba yin mubaya’a ga jami'an gwamnati da ke zaune a cikin ofisoshin su ba, saboda haka take shawartar jami’an tsaro dasu dauki mataki cikin gaggawa na zuwa har inda yan ta'addan suke don magance matsalar.

Ta kara da cewa indan har aka samu wadanda za suyi magana da su, tana da tabbacin cewa zasu saurare su kuma hare-hare zai tsaya don su ma mutane ne kamar kowa kuma suna son zaman lafiya.

KU KARANTA: Sakacin gwamnatin APC ne ya janyo Boko Haram suka sace 'yan matan Dapchi - Atiku

Ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da Jaridar Punch a kan yan matan makarantar sakandare na Dapchi da aka sace kwanannan. Ta kuma bayyana cewa yan kungiyar addinin musuluncin sune fushi ne kan yadda jami'an tsaro ke halaka musu 'yan uwa.

Tace wannan abun dake faruwa yana sosa mata zuciya sosai, "yarannan da basu san ma me sukeyi ba wandansu ma ba’ako haifesu ba lokacin da wadannan matsaloli suka fara tasowa," inji ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel