Rayuka 4 sun salwanta a wani mummunan hatsari da ya afku a garin Abuja

Rayuka 4 sun salwanta a wani mummunan hatsari da ya afku a garin Abuja

Hukumar tsaro ta kiyaye manyan hanyoyi ta tabbatar da mutuwar wasu mutane hudu da ta hadar har da wani soja guda a wani mummunan hatsari da ya afku a mararrabar Nyanya dake daura da hanyar Abuja zuwa Keffi.

Kakaki hukumar , Mista Bisi Kazeem, shine ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai a garin Abuja, inda yace an samu mutane 10 da suka raunata sakamakon hatsarin da ya afku a safiyar ranar Juma'ar da ta gabata.

Rayuka 4 sun salwanta a wani mummunan hatsari da ya afku a garin Abuja

Rayuka 4 sun salwanta a wani mummunan hatsari da ya afku a garin Abuja

Kazeem ya bayyana cewa, wannan mummuna hatsari ya afku a tsakanin motoci 15 da wani babur guda daura da gadar Karu da Nyanya da misalin karfe 9.30 na safiya.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Rubutun 'Allahu Akbar' ya bayyana jikin wani itace a jihar Legas

A cewar sa, mutanen da suka riga mu gidan gaskiya sun hadar da maza biyu, mace daya tare da na goye guda.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma fadar sa ta Villa bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Filato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel