Ziyarar da Buhari zai kawo Benuwe alama ce na kawo karshen kashe-kashe a jihar - Ortom

Ziyarar da Buhari zai kawo Benuwe alama ce na kawo karshen kashe-kashe a jihar - Ortom

- Gwamnan jihar Bunue Samuel Ortom yace zuwan Buhari jihar a sati mai zuwa zai magance matsalar tsaro a jihar

- Ortom ya fadi zancen ne a wurin wani taro na mika tallafin gwamnati ga sansanin yan gudun Hijira, daga kwamitin tarayya zuwa ga gwamnatin jiha

- Gwamnan yayi godiya ga Kwamitin Tarayya na shugaban kasa da samar ma wadanda fadan Filani ya shafa wurin zama da abinci

Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom yace ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai a Jihar tasu ranar Litinin mai zuwa, zata taimaka wurin magance matsalar tsaro na har abada a jihar.

Ortom ya bayyana hakan ne, a wurin wani taron mika tallafin gwamnatin tarayya ga sansanin ya gudun hijira na Abagana daga kwamitin tarayya zuwa gwamnatin jiha. Sakamakon haka, itama gwamnatin jiha ta haka rijiyar burtsatse guda uku a cikin sansanin a matsayin karin nata tallafin.

Ziyarar Buhari Jihar Benue alama ce ta kawo karshen kashe-kashe - Ortom

Ziyarar Buhari Jihar Benue alama ce ta kawo karshen kashe-kashe - Ortom

KU KARANTA: Rashin tausayi: Wani mutum a kasar Indiya ya watsa wa matar sa guba don ta haifi mace

Ya kuma yi godiya ga jama’ar gari da suka bada tallafin abubuwa da dama don cigaba da tafiyar da sansanin, ya kuma roki Ubangiji da ya basu lada.

Wakilin Ciyaman din kwamitin tarayya, Mr. John Owoicho, ya mika lambar yabo ga gwamnatin jihar bisa ga kokarin da takeyi na daukar mataki idan masifa ta auku, yace jihar ta Benue tana kan gaba ta wannan fannin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel